Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da janye shirin da yake yi na kafa wata rundunar tsaro ta ƴan sa kai mai suna Hisba Fisabilillah.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Baffa Babba Ɗan Agundi, shugaban kwamitin kafa Hisbar a ƙarƙashin Ganduje, ya fitar a ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa an cimma matsayar janye shirin ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
A cewar sanarwar, an sauya matsayar ne sakamakon martanin jama’a da kuma damuwa da ruɗani da shirin ya janyo a faɗin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, masu ruwa da tsakin sun yanke shawarar dakatar da shirin kafa rundunar domin bai wa gwamnatin jihar Kano damar sake duba batun korar ma’aikatan Hisba, tare da warware matsalar ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Matakin na Ganduje ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan makomar Hisba da rawar da take takawa wajen tabbatar da da’a da tarbiyya a jihar Kano.


