Buhari ya yarda da jita-jitar cewa na shirya kashe shi – Aisha Buhari

0
11

Uwargidan tsohon shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta bayyana yadda marigayi, Muhammadu Buhari, ya fara kulle kansa a ɗaki bayan da ya yarda da wasu jita-jita da ake yaɗawa a fadar shugaban ƙasa cewa ita ce ta shirya kashe shi.

Aisha Buhari ta kuma bayyana cewa rashin lafiyar da ta tilasta Buhari yin hutun jinya na tsawon kwanaki 154 a shekarar 2017 ba ta da alaƙa da guba ko wata cuta mai ban tsoro, sai dai ta samo asali ne daga tangardar tsarin ciyarwa da rashin kula da abinci yadda ya kamata.

Ta ce rashin lafiyar ta fara ne bayan da aka sauya tsarin abinci da karin kumallo da ta saba kula da shi tun lokacin da suke Kaduna, kafin su hau mulki.

Wannan bayani na Aisha Buhari na cikin wani sabon littafi mai shafi 600 mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya rubuta, kuma aka ƙaddamar da shi a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Litinin.

Littafin, wanda ya ƙunshi babi 22, ya kawo tarihin rayuwar Buhari tun daga ƙuruciyar sa a Daura, jihar Katsina, har zuwa karshen rasuwar sa a wani asibiti da ke London a tsakiyar watan Yulin 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here