Tinubu ba ya saka baki a ayyukan hukumar EFCC–Fadar shugaban ƙasa

0
16

Tinubu ba ya saka baki a ayyukan hukumar EFCC–Fadar shugaban ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin wasu manyan ’yan adawa da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) wajen tsananta wa ’yan adawa da kuma raunana dimokuraɗiyyar ƙasa da jam’iyyu da dama.

A wata sanarwa da Mai bawa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, ya bukaci ’yan siyasa da su daina tozarta hukumomin ƙasa, yana mai jaddada cewa EFCC hukuma ce mai cin gashin kanta wadda doka ta kafa.

Sanarwar ta zo ne bayan Atiku Abubakar, Sanata David Mark, Peter Obi da wasu ’yan adawa sun zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da EFCC wajen gallaza wa abokan hamayya.

Onanuga ya bayyana cewa irin wadannan zarge-zarge ba su da tushe, yana cewa ’yan adawar na neman uzuri ne kan gazawar su da kuma juyar da hankalin jama’a domin cimma moriyar siyasa.

Ya ce babu wani ɗan siyasa da aka tilasta masa shiga jam’iyyar APC, yana mai cewa wadanda suka koma jam’iyyar suna ganin irin nasarorin da shirin gyaran tattalin arziki na Shugaba Tinubu ke kawowa.

Fadar Shugaban Ƙasa ta kara da cewa binciken EFCC ya fara tona asirin wasu tsofaffin jami’an gwamnati da ke da bayani da za su yi kan yadda suka tafiyar da dukiyar jama’a a lokacin da suke kan mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here