Matashi ya kashe ladani yayin kiran Sallar Asuba a Kano

0
4

Wani mummunan lamari ya faru a unguwar Hotoro Maraɓa, ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano, inda ake zargin wani matashi ya yanka maƙogaron Ladani yayin da yake tsaka da kiran Sallar Asuba a safiyar Litinin, 15 ga Disamba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a cikin masallaci, inda Ladanin, Malam Kasim, ke kiran sallah. Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun yi ramuwar gayya, inda ake zargin sun kashe matashin a nan take.

Ɗaya daga cikin ’ya’yan Ladanin, Maryam Kasim, ta shaida cewa sun samu gawar mahaifin nasu a masallaci, tare da ganin alamun tashin hankali a wajen, abin da ya jefa iyali da mazauna yankin cikin firgici.

Tuni jami’an tsaro suka mamaye yankin domin kwantar da tarzoma, yayin da matasan unguwar suka fito domin nuna fushin su da rashin amincewa da abin da ya faru.

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Kano bai samu nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, amma ana sa ran za su yi karin bayani nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here