Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa na da cikakken ikon kundin tsarin mulki na ayyana dokar ta-ɓaci a kowace jiha, domin hana rushewar doka da oda ko fadawa cikin rikici da tashin hankali.
A hukuncin da alkalai shida suka goyi baya, yayin da ɗaya ya ƙi amincewa, Kotun Ƙoli ta jaddada cewa kundin tsarin mulki ya bai wa Shugaban Ƙasa damar ɗaukar irin wannan mataki.
Kotun ta kuma yanke cewa, a lokacin dokar ta-ɓaci, Shugaban Ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni, muddin dakatarwar tana da lokacin ƙarewa.
Mai Shari’a Mohammed Idris, ne ya jagoranci yanke hukuncin, inda ya ce Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya bai wa Shugaban Ƙasa ikon ɗaukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a duk inda aka ayyana dokar ta-ɓaci.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da jihohin da jam’iyyar PDP ke mulki suka shigar, suna ƙalubalantar ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Rivers da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, inda aka dakatar da zaɓaɓɓun shugabannin jihar na tsawon watanni shida.
Jihohin da suka shigar da ƙarar sun haɗa da Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa.


