Gowon yana nan bai mutu ba–Adeyeye

0
13

Mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, Adeyeye Ajayi, ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Gowon ya rasu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ajayi ya bayyana labarin a matsayin ƙarya, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar yana raye, kuma yana cikin koshin lafiya.

Ya ce: “Dukkan rahotannin da ke cewa Janar Yakubu Gowon ya mutu ƙarya ce tsagwaronta. Yana raye, yana cikin koshin lafiya, kuma har yanzu yana gudanar da rayuwa.”

Ajayi ya ƙara da cewa Gowon na ci gaba da halartar tarukan jama’a tare da bada gudunmawa a tattaunawar da ta shafi zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da ci gaban Najeriya.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yaɗa labaran da ba a tantance ba, domin irin haka na haddasa firgici da damuwa ga jama’a da iyalan mutum.

A karshen makon da ya gabata ne jita-jitar mutuwar tsohon shugaban ƙasar ta bazu a shafukan sada zumunta, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin rudani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here