Cece kuce ya mamaye shirin ɗauke shalkwatar bankin masana’antu daga Abuja zuwa Lagos

0
20

Shirin gwamnatin tarayya na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu (BOI) zuwa Eko Atlantic City a Jihar Lagos ya tayar da kura, inda masana da ‘yan kasa ke nuna damuwa kan muhimmancin wannan mataki.

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da gina sabuwar shalkwatar bankin a Eko Atlantic, kamar yadda ƙaramin ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Sanata John Enoh ya bayyana. Ya ce sabuwar shalkwatar za ta taimaka wajen faɗaɗa rawar bankin BOI wajen tallafa wa masana’antu, kananan da matsakaitan sana’o’i (SMEs), da fitar da kayayyaki waje.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa BOI na da ofisoshi masu yawa tun tuni a Lagos da Abuja, ciki har da babbar shalkwata a Marina da kuma gini mai hawa 12 da aka kammala a Abuja a 2022, wanda har wasu sassa ake bayarwa haya.

Masana tattalin arziki da masu sharhi kan harkokin jama’a na cewa kashe biliyoyin naira wajen gina wata sabuwar hedkwata a Eko Atlantic, inda farashin fili ke kaiwa dala $1,500 zuwa $3,000 a kowanne murabba’in mita, na iya zama almubazzaranci, musamman a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasa ke fuskantar ƙalubale.

Sun yi kira da a karkatar da irin wannan kuɗi zuwa tallafa wa ƙananun masana’antu, manoma da kamfanoni, domin rage rashin aikin yi da bunƙasa tattalin arziki, maimakon gina wuri mai tsada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here