Waiya ya Ƙaddamar da Ofishin ‘Yan Jarida Masu Wallafa Labarai a Yanar Gizo

0
8

Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ƙaddamar da ofishin ƴan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo ta jihar Kano.

Kamarade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce wannan mataki na nuna amincewar gwamnati da muhimmancin kafafen yaɗa labarai na yanar gizo a sadarwa da al’umma. Ya tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da kula da walwalar ‘yan jarida da horas da su.

An ƙaddamar da ofishin ne a ranar Asabar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ da ke Kano, yayin rufe bikin Makon Yan Jarida na na shekarar 2025 da NUJ ta jihar Kano ta shirya.

Shugaban NUJ na ƙasa, Kamarade Alhassan Yahaya, ya ce ƙaddamar da ofishin zai ƙarfafa ƙwarewa, haɗin kai da bin ƙa’idojin aikin jarida a tsakanin ‘yan jaridar yanar gizo. Ya bayyana cewa aikin jarida na zamani na da matuƙar muhimmanci, tare da kira ga ‘yan jarida su riƙa aiki da gaskiya da kuma kwarewa.

Ya yaba wa NUJ ta jihar Kano bisa jagoranci na bai ɗaya da shirye-shiryen da suka dace da sauye-sauyen da ke faruwa a fannin yaɗa labarai. 

Tun da farko, Shugaban kungiyar ƴan jarida ta ƙasa reshen jihar Kano, NUJ, Kamarade Sulaiman Dederi, ya ce ofishin zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai, daidaita aiki, da bunƙasa hulɗa a tsakanin ‘yan jarida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here