Mata a yankin arewa sun roƙi Turji ya miƙa wuya kafin lokaci ya ƙure masa

0
9

Wata ƙungiyar mata daga Arewa maso Yamma ta yi kira ga fitaccen ɗan bindiga Bello Turji da ya ajiye makamai ya rungumi zaman lafiya, domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta daɗe tana damun yankin.

Kiran ya biyo bayan wani samame da sojojin Najeriya suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto, inda aka kashe babban mataimakin Turji, Kallamu Buzu, tare da wasu ‘yan bindiga.

Matan sun bayyana wannan kira ne a birnin tarayya Abuja, bayan sun gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya, tare da yi wa sojojin ƙasa addu’ar samun kariya da nasara.

Da take magana a madadin ƙungiyar, Salamatu Bello, ta ce al’ummar yankin sun gamsu da yadda sojoji ke tunkarar matsalar ‘yan bindiga cikin natsuwa da ƙarfi. Ta ƙara da cewa a matsayin su na iyaye mata ba za su iya ci gaba da rayuwa cikin tsoro da asarar rayuka ba.

“Muna roƙon Bello Turji da ya mika wuya kafin lokaci ya kure masa,” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here