Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a jihar Kano

0
9

Wani jirgin sama mallakin kamfanin Flybird ya yi saukar gaggawa a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) bayan tayar gaban sa ta lalace yayin sauka.

Majiyoyi daga filin jirgin saman sun tabbatar da cewa fasinjoji 11 da ke cikin jirgin, ciki har da maโ€™aikatan jirgin guda uku, sun fito lafiya kalau ba tare da wani ya ji rauni ba.

Zuwa yanzu an ษ—auke jirgin daga kan hanyar sauka tare da matsar da shi domin gyara, lamarin da ya dawo da harkokin filin jirgin sama yadda ya kamata a Kano.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here