Gwamnatin Tarayya zata samu Naira triliyan 1.9 daga sabon harajin Tinubu a 2026

0
8

Gwamnatin Tarayya zata samu Naira triliyan 1.9 daga sabon harajin Tinubu a 2026

Gwamnatin Tarayyar ta bayyana cewa tana sa ran samun kusan Naira tiriliyan 1.9 daga sabon harajin da ta fito da shi kuma zai fara aiki a shekarar 2026.

Rahotanni daga takardun kasafin kudin 2026 sun nuna cewa ana hasashen gwamnatin za ta tara Naira triliyan 1.899 daga wannan haraji a shekarar 2026.

Hasashen ya kuma nuna cewa kuɗin da za a samu daga harajin zai ƙaru zuwa Naira triliyan 2.41 a 2027, sannan ya kai Naira triliyan 3.13 a 2028, lamarin da ya sa harajin ya zama ɗaya daga cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga mafi saurin bunƙasa a bangaren da ba na man fetur ba.

Sabon harajin yana karɓar kashi 4 cikin 100 na ribar kamfanoni da ake tantancewa, ƙarƙashin Dokar Haraji ta Najeriya ta 2025. 

An tsara harajin zai fara aiki ne daga 1 ga Janairu, 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here