Ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle, ya ƙalubalanci mutanen da ke alaƙan ta shi da yin mu’amala da ƴan ta’addan jihar Zamfara.
Matawalle, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta DCL.
Yace masu yada wannan zargi basu da wata hujja akan hakan, yana mai cewa bita da kullin siyasa ne ya janyo hakan don ana yin zaton zai kuma neman takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓen shekara ta 2027.
Ya kara da cewa har Ila yau akwai masu burin a cire shi daga mukamin ministan tsaro.
Duk wanda yake yin zargin cewa ina yin alaƙa da ƴan ta’adda ko ina taimaka musu, ya kai ni kotu don tabbatar da zargin sa da hujja, amma in ba’a same ni da laifi ba zai biya duk diyyar da na nema a wajen sa, inji Bello Matawalle.
Babu wanda yake tabbatar da zargi sai kotu, inji shi.
A ƴan kwanakin nan dai an samu yawaitar masu zargin Matawalle da yin alaƙa da ƴan bindiga tun a zamanin da yake mulkar Zamfara.


