An ƙone mace mai juna biyu da ƙaramin ɗan ta bayan kashe su a Kano

0
13

Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu a birnin Kano sun shiga firgici da jimami bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe wata mace mai juna biyu tare da ɗan ta mai watanni 18, ta hanyar ƙone su a cikin gidan su.

Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar, inda mijin matar ya dawo gida da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sai ya tarar an kulle gidan daga waje. Bayan ya buɗe ƙofar gidan ta ƙarfi, sai ya gano gawar matar tasa da ta ɗansa a kwance.

Wani jagoran al’umma a yankin, Ahmad Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya koka kan ƙarancin tsaro a unguwar. Ya bayyana cewa al’umma sun haɗa kai sun gina ofishin ‘yan sanda, amma har yanzu ba a tura jami’an tsaro da za su kula da shi ba.

Ya roƙi Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, da ya gaggauta tura jami’ai domin ƙarfafa tsaro da kuma hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta fara bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ta’asa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here