Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake ƙaryata raɗe-raɗin da ke cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, inda ya jaddada cewa ba bi wanda ake kaiwa hari saboda addinin sa.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya tana da alaƙa da dalilai na tarihi, tattalin arziƙi da kuma aikata laifuka, ba wai tsangwama ko kisan addini ba.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake buɗe babban taron shekara-shekara na ƙungiyar Nasrul-Lahi-l-Fatih Society (NASFAT).
Taron ya mayar da hankali ne kan taken: Gina juriyar al’umma a duniya mai canzawa: rawar addini da al’umma.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai domin magance matsalar tsaro da haɗa kan al’umma ba tare da nuna bambanci na addini ba.


