Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP a Borno

0
9
Sojoji
Sojoji

Dakarun sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation HADIN KAI (OPHK) sun yi nasarar daƙile wani harin haɗin gwiwa da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke yankin Mairari a jihar Borno.

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar ta bayyana cewa mayaƙan ISWAP sun yi yunƙurin kutsawa cikin sansanin ne ta hanyar amfani da na’urorin fashewa da aka ɗaura a jikin ababen hawa.

Sanarwar ta ce dakarun sojin sun gano na’urorin fashewar tun da wuri, inda suka kawar da su tare da hana mayaƙan samun damar shiga sansanin.

Rahoton ya ƙara da cewa faifan bidiyo da hotunan CCTV sun tabbatar da kashe mayaƙan ISWAP da dama, yayin da wasu suka samu munanan raunuka a lokacin musayar wuta.

Daga cikin kayayyakin da sojoji suka ƙwato daga hannun mayaƙan akwai bindigogi ƙirar AK-47, harsasai, gurnetin hannu, babura da kuma na’urorin sadarwa.

A halin yanzu, dakarun sojin na ci gaba da gudanar da sintiri da ayyukan tsaro a yankin domin daƙile duk wani yunkurin hare-hare tare da tabbatar da tsaron al’ummar yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here