Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage ranar yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ke yi da dakataccen jami’in ɗan sanda, DCP Abba Kyari, zuwa ranar 26 ga Fabrairu, 2026.
NDLEA na zargin Abba Kyari, tsohon shugaban rundunar ’yan sanda masu yaƙi da garkuwa da mutane (IRT), tare da ’yan uwansa biyu, da ƙin bayyana ainihin kadarorin su da kuma juya kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya.
A zaman kotun na ranar Juma’a, Mai shari’a James Omotosho ya sanya ranar bayan ɓangarorin da ke cikin shari’ar sun kammala gabatar da hujjoji da muhawara ta hannun lauyoyin su.
A cewar NDLEA, bincikenta ya gano kadarori 14 da ake zargin mallakar Abba Kyari ne, ciki har da, manyan shaguna, gidaje, filaye da gonaki.
Haka kuma, hukumar ta ce ta gano sama da Naira miliyan 207 da kuma Yuro 17,598 a asusun bankuna daban-daban da ake dangantawa da Abba Kyari, ciki har da GTBank, UBA da Sterling Bank.
NDLEA ta ce duk waɗannan ayyuka sun saɓa wa Dokar NDLEA da kuma Dokar Hana Safarar Kuɗaɗe.
Abba Kyari dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa ta bakin lauyan sa inda yace ya bayyana kadarorin sa da na matar sa bisa tanadin doka, sannan ya ce ba shi da alaƙa da wasu kadarorin da NDLEA ke dangantawa da shi.


