EFCC ta musanta kalaman Abubakar Malami dangane da hana shi beli
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta ce tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), bai cika sharudan belin da aka ba shi ba, sabanin ikirarin da ya yi cewa an soke belin sa saboda halartar taron siyasa a Kebbi.
EFCC ta bayyana cewa an bawa Malami beli na wucin gadi bayan yi masa tambayoyi a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, bisa sharudda guda biyar, amma bai cika ko ɗaya daga cikinsu ba.
Hukumar ta ce ko da yake ya nemi jinkiri saboda rashin lafiya, sai dai bai gabatar da sahihin rahoton likita kan lafiyar tasa ba.
Saboda haka, EFCC ta ce an tsare Malami har sai ya cika dukkan sharudan belin, tana mai ƙaryata zargin cewa ta hana shi shiga harkokin siyasa ko magana da kafafen yaɗa labarai.


