An Fara Kada Kuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomin jihar Borno

0
9

An fara kada ƙuri’a a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar Borno a safiyar yau Asabar.

Zaɓen na gudana ne domin zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 27 da kuma kansiloli 312 a fadin ƙananan hukumomi da mazabu 312 na jihar.

Jam’iyyun siyasa guda shida ne ke cikin takardun zaɓe da aka gani a rumfunan kada ƙuri’a. Jam’iyyun sun haɗa da APC, Boot Party, Labour Party (LP), Peoples Redemption Party (PRP), New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kuma Social Democratic Party (SDP).

A ranar Juma’a, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da janyewa daga zaɓen, tana mai cewa ba ta yarda da sahihanci da adalcin hukumar zaɓe ba, tare da zargin tsadar kuɗin fom ɗin tsayawa takara.

PDP ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno (BOSIEC) da rashin samar da yanayi mai gamsarwa ga jam’iyyun adawa dangane da gaskiya da amincin zaɓen.

Da yake mayar da martani, shugaban BOSIEC, Tahir Shettima, ya ce hukumar ba za ta tilasta wa kowace jam’iyya shiga zaɓe ba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here