Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa matsalar rashawa a Najeriya ta yi tsanani matuƙa wanda har idan aka yi amfani da dokokin ƙasa yadda ya kamata, kashi 80% na ‘yan ƙasa na iya tsintar kansu a gidan yari, saboda aikata wannan laifi.
Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku, ne ya bayyana haka a taron horas da shugabannin kananan hukumomi, inda ya ce rashawa ta mamaye kusan dukkan bangarorin rayuwar Najeriya saboda raunin hukumomi da ƙarancin gaskiya a gudanar da aiki.
Ishaku ya yi nuni da cewa rashawa ta janyo raguwar ci gaba, ta ƙara talauci, ta kuma haddasa tashe-tashen hankula a faɗin ƙasa. Ya kuma soki shugabannin kananan hukumomi da ke kammala wa’adin aiki ba tare da wani aikin ci gaba da za su nuna ba.
Ya ce hukuncin da ake yankewa manyan masu cin rashawa ba mai tsauri ba ne, inda ya bayar da misalin wanda ya sace Naira biliyan biyu 2, amma aka yanke masa hukuncin shekaru biyar kawai, yana mai kira da a tsaurara dokokin yaƙi da rashawa.
A nasa bangaren, Kwamishinan Kananan Hukumomi na Kaduna, Sadiq Mamman Legas, ya yi tir da halin da jama’a ke nuna na lalata kayan gwamnati, yana mai bayyana cewa ma’aikatarsa ta yi tanadin sama da Naira biliyan 8 wurin gyaran hasken wutar lantarki a wasu yankuna, amma al’ummomin da aka yi wa aikin suka lalata kayan.


