Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar Filato ta tabbatar da mutuwar daliban Jami’ar Jos takwas a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a safiyar yau Alhamis.
Lamarin ya auku ne misalin ƙarfe 2:00 na dare a titin Jos zuwa Zaria, inda motar da ɗaliban ke ciki ta yi karo da wata babbar motar kaya, abin da ya janyo mummunan raunuka da asarar rayuka.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗaliban na kan hanyar su ta komawa ɗakunan kwana bayan shaƙatawar dare lokacin da haɗarin ya ritsa da su. An garzaya da sauran waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa da wajen da aka yi hatsarin, domin samun kulawar gaggawa, inda mutum biyu ke ci gaba da karɓar magani.
Kakakin FRSC a jihar ya ce an kaddamar da bincike domin gano musabbabin faruwar hatsarin, tare da jan hankalin direbobi su kula da tuƙin ganganci musamman a lokutan dare domin kauce wa irin waɗannan manyan haɗurra.


