Jaridar Punch, ta rawaito cewa gwamnatin Tarayya na shirin ciwo bashin Naira 17.89 tiriliyan a 2026 domin cike gibi a kasafin kuɗi, na shekarar 2026, bayan hasashen samun kuɗaɗen shiga ya ragu sosai. Wannan adadin ya karu da kashi 72% idan aka kwatanta da Naira 10.42 tiriliyan da aka aro a 2025.
Bayanan kasafin sun nuna cewa gibin kasafin 2026 zai kai Naira triliyan 20.12 a 2026, ɗaga Naira triliyan 14.10 na bana.
Jaridar ta ce an yi hasashen cewa kuɗaɗen shiga kuma za su yi ƙasa zuwa Naira triliyan 29.35, lamarin da ya janyo bukatar karin bashi.
Saboda haka, gwamnati za ta dogara da bashin cikin gida Naira na Naira triliyan 14.31 da na waje Naira triliyan 3.58 don aiwatar da kasafin.


