Hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta Kano SUBEB, ta sanar da shirin ɗaukar ƙarin malamai 4,000 domin inganta karatun lissafi da turanci a matakin farko.
Shugaban hukumar, Yusuf Kabir, ya bayyana haka a taron nazarin sakamakon karatu na 2025 da aka gudanar a Kano, tare da goyon bayan shirin PLANE na gwamnatin Birtaniya. Ya ce duk da ɗaukar malamai 4,343 a baya-bayan nan, jihar na fama da ƙarancin malamai a kananan hukumomi da dama.
Kabir, wanda Sakatariyar SUBEB Hajiya Amina Umar ta wakilta, ya ce ana kammala shirye-shirye a cibiyoyin na’ura mai ƙwaƙwalwa bakwai da ke Wudil, Bichi da wasu yankuna domin gudanar da jarabawar gano ƙwarewar masu neman aikin.
Yanzu haka, wasu makarantu na da malami ɗaya ga ɗalibai 132, lamarin da hukumar ke son ragewa zuwa ɗalibai 60 kan malami ɗaya.


