Gwamnatin Kano ta nemi haɗin kan ƴan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo kan sha’anin tsaro
Gwamnatin jihar Kano, ta nemi haɗin kan ƴan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, domin su cigaba da tallafa mata wajen bayyana sahihan bayanai a musamman a sha’anin tsaro.
Kwamishinan Ma’aikatar yaɗa labarai da al’amuran cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya nemi hakan ya ranar Alhamis, yayin da ya jagoranci wata tattaunawa ta musamman tare da mambobin kungiyar ƴan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, wanda ya gudana a ma’aikatar yaɗa labarai ta Kano.

Waiya, yace hakan ya zama wajibi domin bayyanawa al’ummar Kano sahihan labarai yayin da ake fuskantar rashin tsaro a wasu yankunan jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana damuwar sa a kan yadda yace a kwanakin baya wata kafar yaɗa labarai a yanar gizo ta wallafa labarin dake bayyana jihar Kano a matsayin wata jihar da take da dandazon ƴan ta’adda, yana mai cewa hakan ba gaskiya bane kuma ba daidai bane.
Kamata ya yi a haɗa hannu da gwamnati domin yaƙar rashin tsaro ba yin amfani da kafafen yaɗa labarai domin yayata ayyukan rashin tsaro ba, saboda hakan yana da illa mai yawa, inji Waiya.
Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai a yanar gizo, na da muhimmanci a wanann zamani sakamakon cewa suna aikewa da saƙo ga miliyoyin mutane a ƙanƙanin lokaci, kuma a kowanne lokaci.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ƴan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, Abubakar Abdulkadir Ɗangambo, ya yi alkawarin cewa zasu bada gudunmawa wajen kiyaye wallafa duk wani labarin da ba zai taimaka wajen goyon bayan rashin tsaro a jihar Kano ba.


