Gwamnan Kano ya naɗa sabuwar shugabar jami’ar Northwest

0
18

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Farfesa Amina Salihi Bayero a matsayin cikakkiyar Shugabar Jami’ar Northwest, na tsawon shekaru biyar, wanda naɗin ya fara aiki daga 1 ga Disamba, 2025.

Wannan sanarwa ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya ce nadin ya biyo bayan zaben da Kwamitin Gudanarwar Jami’ar ya gudanar bisa tsauraran ka’idojin tantancewa.

Gwamna Yusuf ya yaba da yadda shugabannin jami’ar suka gudanar da zaɓen bisa adalci da cancanta, sannan ya nemi addu’o’in samun taimakon Allah ga sabuwar shugabar.

Farfesa Amina, ta rike manyan mukamai daban-daban a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here