Tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, ya kwashe kwanaki biyu a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) yayin da ake ci gaba da binciken sa kan zargin aikata manyan laifuka 18, ciki har da almundahanar kuɗaɗe da kuma tallafawa ƴan ta’adda.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa EFCC ta sami umarnin kotu na cigaba da tsare Malami, yayin da ake tuhumar sa kan yadda aka rasa takardun bayanin dawowar dala miliyan $346.2 na kudin Abacha daga Switzerland da kuma wasu kuɗaɗen da aka dawo dasu Najeriya daga tsibirin Jersey.
Haka kuma ana binciken sa kan yadda aka fitar da Naira biliyan 4 na shirin tallafin manoma mai suna Anchor Borrowers na Babban Bankin Najeriya (CBN), da zargin zuba Naira biliyan 10 a cibiyoyi kamar makarantu, otal-otal a jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce Malami ya kasa cika sharuddan samun beli zuwa daren Talata, lamarin da ya sa aka cigaba da tsare shi. A halin yanzu ana kuma duba asusun banki 46 da ake zargin suna da alaƙa da shi.
Zuwa yanzu dai EFCC ba ta fitar da sanarwa kai tsaye game da binciken ba.


