Shahararren lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), ya ja hankalin gwamnati cewa dole ne ta magance matsalolin da suka dabaibaye rayuwar ’yan ƙasa idan har ana son kaucewa irin matsalolin siyasa da wasu ƙasashen Afirka ke fuskanta.
Yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Falana ya bayyana cewa talauci mai tsanani, matsalar tsaro da takura ’yancin jama’a na daga cikin abubuwan da kan haifar da yanayin da ke kaiwa ga juyin mulki.
A cewar sa, dimokuraɗiyya ba za ta yi wani tasiri ba muddin gwamnati na ci gaba da matsa lamba ga ’yan adawa ko kuma tana hukunta mutane saboda sun bayyana ra’ayoyin su.
Falana ya bukaci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da ta bude fagen siyasa ga jam’iyyun da ke da manufofi daban-daban, yana mai cewa rashin karfin ’yan adawa shi ne yake sa wasu shugabanni a Afirka su shiga hanyar danniya, wanda daga bisani ke haddasa tashin hankali.
Ya yi nuni da cewa duk lokacin da gwamnati ta gaza kare ’yancin jama’a ko ta toshe hanyoyin shiga siyasa, matsalolin hakan ka iya rikidewa zuwa juyin mulki.
Falana ya kuma jaddada bukatar Najeriya ta zama abin koyi a Afirka ta hanyar kafa tsarin mulki da ke tabbatar da adalci, tsaro da ci gaban jama’a.
Wannan gargadi nasa ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka dakile a Jamhuriyar Benin, wanda dakarun ECOWAS suka shiga tsakani.


