Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wa Majalisar Dattawa da wasiƙa yana neman amincewar ’yan majalisa domin tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar a zaman da aka gudanar ranar Talata.
A cewar Tinubu, bukatar ta biyo bayan roƙon gaggawa da gwamnatin Benin ta yi na samun tallafin rundunar sojin sama ta Najeriya, bayan wani yunƙurin kifar da gwamnati da ake yi a ƙasar.
Ya ce halin da ake ciki a Benin na buƙatar taimakon gaggawa musamman ganin yadda yunƙurin juyin mulkin ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiyar kasar.
Tinubu ya kuma jaddada cewa, kasancewar Najeriya da Benin suna da ƙarfin alaƙa da kuma ka’idar tsaron haɗin gwiwa da ECOWAS ke bi, ya zama wajibi Najeriya ta tallafa.
Bayan karanta wasiƙar, Majalisar Dattawa ta miƙa batun ga wani kwamitin ta domin daukar mataki cikin gaggawa.


