Nijar ta sanya takunkumi a kan kayayyakin da suke shiga ƙasar daga Najeriya

0
14

Hukumar mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta sanar da sanya sabbin takunkumi kan dukkan kayan da ke shiga ƙasar daga Najeriya, tana mai cewa an dauki matakin ne saboda ƙarin damuwa kan batun tsaro a yankin.

Sanarwar, wacce babban jami’in Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta ƙasar, Kanal Mohamed Yacouba Siddo, ya fitar, ta bukaci a rika binciken kayan da suka fito daga Najeriya kafin a ba su izinin ci gaba da tafiya.

Matakin ya biyo bayaan yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, da kuma zarge-zargen da ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta yi cewa sojojin Najeriya 11 an tsare su a Burkina Faso saboda karya dokar sararin samaniyar ƙasar.

Sai dai rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa jirgin ta ya yi saukar gaggawa ne saboda matsalar fasaha, ba wai ya take doka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here