Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu ta tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen daidaita al’amuran tsaro da kare dimokuraɗiyya a ƙasar.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta bukatar shugaban ƙasa a yau Talata, sannan ‘yan majalisa suka shiga zaman sirri don nazarin tasirin hakan, ciki har da yiwuwar kwararar ‘yan gudun hijira da barazana ga yankunan kan iyaka idan rikici ya ƙara ta’azzara a Benin.
Bayan tattaunawa, majalisar ta kada kuri’ar amincewa, kuma yawancin sanatoci suka goyi bayan a tura sojojin, suna bayyana matakin a matsayin kariya ga muradun Najeriya da tsaron ta.
Akpabio ya ce matakin zai taimaka wajen hana kifar da gwamnati a Benin tare da tabbatar da zaman lafiya a yammacin Afirka.


