Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta tsare

0
7

Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta kama bayan jirgin sojojin samfurin C-130, wanda ya yi saukar gaggawa ba tare da izini ba a Bobo Dioulasso.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron Burkina Faso sun tsare sojojin tun ranar Litinin, bayan Æ™ungiyar Æ™asashen sahel AES wadda ta Æ™unshi Burkina Faso, Mali da Nijar ta bayyana saukar jirgin a matsayin keta hurumin sararin samaniyar ta. 

Shugaban AES, Assimi Goïta, ya yi jan kunnen cewa za a ɗauki tsauraran matakai kan irin haka a nan gaba.

Sai dai a ranar Talata, hukumomin tsaro na Burkina Faso suka tabbatar da sakin sojojin bayan gudanar da tambayoyi. An ba su izinin barin ƙasar, lamarin da ya rage ƴar takaddamar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A nata bangaren, Najeriya ta bayyana cewa jirgin na kan hanyar sa ta zuwa Portugal domin wani aiki, amma ya yi saukar gaggawa ne sakamakon matsalar fasaha. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here