Tinubu Ya Yaba Wa Sojojin Nijeriya Kan Dakile Shirin Juyin Mulki a Benin

0
5
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin Najeriya bisa gaggawar da suka nuna wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan gwamnatin ƙasar ta yi kira ga Najeriya da ta kawo mata ɗauki.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin Benin ta nemi goyon bayan Najeriya sau biyu domin kare dimokuraɗiyyar da ta shafe shekaru 35 tana aiki.

Sanarwar ta ce Tinubu ya amince da bukatar ne bayan hukumomin Benin sun tabbatar da cewa wasu mayakan da ke ikirarin kifar da gwamnati sun mamaye gidan talabijin na ƙasar tare da taruwa a wani sansanin soja.

A matakin farko, Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta Najeriya da ta shiga sararin samaniyar Benin domin taimakawa jami’an tsaron ƙasar wajen fatattakar masu tawaye da kuma tabbatar da tsaron muhimman cibiyoyi.

Daga nan, Benin ta sake neman taimakon Najeriya ta fuskar tattara bayanan sirri da kai agajin gaggawa ta jiragen sama bisa jagorancin hukumomin tsaron ƙasar.

Hakazalika, gwamnatin Benin ta nemi a tura dakarun ƙasa na Najeriya domin gudanar da ayyuka na musamman da nufin kare tsarin mulki da kuma dakile kowace kungiya da ta dauki makamai a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here