Wani rikicin da ya dade yana faruwa tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Yelwan Musari na ƙaramar hukumar Guri, jihar Jigawa, ya sake kunno kai a ƙarshen mako, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
An tabbatar da mutumin da ya rasu da sunan Magaji Mai’aya, wanda mazauna yankin suka bayyana shi a matsayin mai noman gargajiya.
Shaidu a kauyen sun ce an yi ta samun tashin hankali tun watanni da suka gabata, bayan tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu ta gaza taka rawa.
Ado Musa, wani mazaunin yankin, ya ce rikicin ya barke ne bayan wasu da ake zargi makiyaya ne suka kai farmaki tsakanin ranar Asabar da Lahadi, inda suka kona gidaje da injunan aikin shinkafa.
Ya ce maharan sun tare hanyar Guri zuwa Hadejia, lamarin da ya hana wadanda suka jikkata samun gaggawar kulawa a Asibitin Hadejia.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, wani ɗaya ya ɓace, yayin da biyu suka jikkata, ciki har da jami’in tsaro. Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce an tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin.


