Wani bangare na jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC), tare da kafa sabon kwamitin rikon kwarya.
An kaddamar da kwamitin mai mambobi 13 a ranar Lahadi, yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa NEC da aka gudanar a gidan Wike da ke Abuja. Kwamitin zai shugabanci jam’iyyar na tsawon kwanaki 60 kafin a gudanar da sabon babban taron ƙasa.
Abdulrahman Mohammed ne ke jagorantar kwamitin, yayin da Samuel Anyanwu ya zama sakatare. Wasu mambobin sun haɗa da Kamaldeen Ajibade, Umar Bature, Kyari Grema, Janguda Mohammed, Okechukwu Osuana, Nwogu Olaka, Sandy Onor, Adenike Ogunse, Bisi Kolawole, Deji Doherty da Ibrahim Aboki.


