Yan sanda sun saki Muhuyi Magaji Rimin-Gado

0
8

An saki tsohon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barrister Muhuyi Magaji Rimin-Gado, daga hannun ‘yan sanda bayan kwana ɗaya da kama shi.

Muhuyi Magaji ya shaida wa SolaceBase cewa an sako shi, amma an umarce shi da ya koma Abuja ranar Litinin domin kammala cika sharuddan belin sa.

An kama shi ne a ranar Juma’a sannan aka tafi da shi zuwa Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an shigar da ƙorafe-ƙorafe biyu a kansa daga tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da kuma tsohon Manajan Daraktan KASCO, Bala Inuwa.

A cikin korafin Ganduje, ya zargi Muhuyi da amfani da matsayinsa wajen aiwatar da tuhuma ba bisa ka’ida ba kan kadarorin gwamnatin Kano a Dala Inland Dry Port, wanda ake zargin ya Ganduje ya mallakawa kansa da ‘ya’yansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here