Jirgin sojojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Neja

0
6

Rahotanni daga jihar Neja sun tabbatar da cewa wani jirgin yaki na rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde, cikin ƙaramar hukumar Borgu.

Wani shafin kafar yaɗa Labarai na cikin jihar, Lapai TV, ya wallafa cewa matukan jirgin biyu sun samu damar ficewa daga cikin jirgin kafin ya faɗi. Wannan na cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon daƙiƙa 57 da aka saki a daren Asabar.

Wani ganau ya bayyana cewa jirgin na iya kasancewa ya tashi ne daga sansanin sojin saman Kainji kafin faruwar lamarin.

Ya ce: “Mun samu labarin cewa rundunar sojin sama ta tura jami’anta zuwa wurin da hatsarin ya faru.”

Wani mazaunin yankin, Lukman Sulaiman, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:10 na yamma. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here