Mun kashe Naira biliyan 100 wajen kula da tsaron Borno a shekara guda–Zulum

0
5

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekarar ta 2025 domin aiwatar da muhimman manufofin tsaro a fadin jihar.

Zulum ya fadi hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Uba, Alhaji Ali Ibn Mamza, biyo bayan harin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a yankin dake kusa da Askira/Uba.

Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro da mazauna yankin bisa nasarar ceto mata manoma 12 da aka sace, tare da cewa ziyarar ta kuma baiwa gwamnati damar tantance halin da ake ciki domin daukar kwararan matakai.

A nasa bangaren, Sarkin Uba ya gode wa gwamnan bisa jajircewar sa wajen kawo ci gaba a yankin, yana mai cewa:

> “Da ba don kokarinka ba, da al’amura sun fi haka muni. Mun yaba da ayyukan da ka yi, kuma da dokar kasa za ta ba da dama, da mun nemi ka cigaba da mulki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here