Gwamnatin Kano ta bayyana waɗanda zasu cigaba da yin goyo a babur mai ƙafa biyu

0
6

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa dokar da ta haramta daukar fasinja da babura ta shafi masu sana’ar achaba ne kawai, ba ta shafi masu amfani da baburan LIFAN ba.

Wannan jawabi ya fito ne daga Kwamishinan Shari’a na jihar yayin wata ganawar aiki da Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bakori, inda suka tattauna kan yadda za a aiwatar da dokar cikin adalci da tsari.

Kwamishinan Shari’a ya ce an dauki matakin ne domin magance barazanar tsaro da ta bayyana a birnin Kano sakamakon yawaitar amfani da achaba wajen aikata laifuka da haifar da cinkoso a manyan hanyoyi. Ya jaddada cewa masu LIFAN za su ci gaba da zirga-zirga da goyon biyu muddin suna bin ƙa’idojin doka da tsaron hanya.

A nasa ɓangaren, CP Bakori ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta yi aiki da umarnin tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen aiwatar da shi. Ya ce duk mai karya dokar hana achaba zai fuskanci hukunci, yayin da masu LIFAN za su ci gaba da harkokinsu ba tare da wani cikas ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here