Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da ginin sabon titin kilomita biyar da zai inganta harkokin sufuri da ci gaban masarautar Gaya.
Jawabin hakan na cikin sanarwar da Mai Magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
An kaddamar da aikin ne a fadar Sarkin Gaya bayan Gwamna Abba ya kai gaisuwar ban girma ga Sarkin, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir. Gwamnan ya umarci kamfanin da ke aikin da ya tabbatar da bin dukkan ka’idojin kwangila domin gina titin mai inganci
Gwamna Abba ya bayyana cewa titin zai haɗa da fitilu masu amfani da hasken rana da kuma ingantattun magudanan ruwa.
Ya kuma shawarci al’ummar Gaya da su ci gajiyar sabuwar Kwalejin Kimiyya da aka kafa a yankin, yana mai cewa ilimi shi ne ginshikin cigaban al’umma.
A nasa jawabin, Sarkin Gaya ya gode wa gwamnatin jihar Kano, kan ayyukan ci gaba da ta ke aiwatarwa, yana mai cewa kusan kashi 80 cikin 100 na alkawuran da Gwamna Abba, ya yi sun cika.


