Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki matakin da shugaban ƙasa Tinubu, dauka na naɗa tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, a matsayin jakada.
Atiku ya bayyana cewa babu wani dalili mai karfi da zai tabbatar da dacewar wannan zabi, sannan kuma hakan yana iya kara raunana amincewar jama’a ga gwamnati.
Atiku ya ce wannan mataki zai sa al’umma su dauki nadin a matsayin wata alaka ta siyasa, ba wai saboda cancanta ko nagarta ba. Ya bayyana hakan a matsayin abin da zai iya ƙara wa gwamnati nauyin matsalar rashin yarda daga al’umma.
Ya kara da cewa naɗa Farfesa Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓen da ake cewa ya kasance mafi rikicewa a tarihin demokradiyyar kasar nan, na aika da saƙo mai muni ga INEC. A cewarsa, hakan na iya nuna cewa “duk da jagorantar zaɓe cikin rudani ko rashin gaskiya, mutum na iya samun babban muƙami daga baya”.
Atiku ya jaddada cewa bai dace wanda ya jagoranci zaɓen da aka yi ta sukar ingancin sa ya amfana da irin wannan sakamako ba.
Ya kammala da cewa irin wannan mataki ba ya karfafa dimokuraɗiyya, balle ya tabbatar da martabar ta da jama’a ke muradin gani.


