Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

0
8

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, tare da wasu mambobi 15, sun sanar da ficewar su daga jam’iyyar PDP zuwa APC a zaman majalisar da aka gudanar ranar Juma’a.

Amaewhule ya bayyana cewa sun yanke wannan shawarar ne saboda “rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP,” wanda ya ce ya shafi haɗin kan jam’iyyar a jihar.

Jihar Rivers dai ta sha fama da rikicin siyasa musamman tsakanin gwamnan jihar Fubara, da mambobin majalisar dokokin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here