Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, tare da wasu mambobi 15, sun sanar da ficewar su daga jam’iyyar PDP zuwa APC a zaman majalisar da aka gudanar ranar Juma’a.
Amaewhule ya bayyana cewa sun yanke wannan shawarar ne saboda “rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP,” wanda ya ce ya shafi haɗin kan jam’iyyar a jihar.
Jihar Rivers dai ta sha fama da rikicin siyasa musamman tsakanin gwamnan jihar Fubara, da mambobin majalisar dokokin.


