Tinubu ya sake naɗa sabbin jakadu

0
9
Tinubu
Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika da sabon jerin sunayen jakadu ga majalisar dattawa domin tantancewa.

Shugaban ya zaɓi tsohon sanata Ita Enang, tsohuwar uwargidan gwamnan Imo Chioma Ohakim, da kuma tsohon ministan cikin gida da tsohon babban hafsan rundunar sojoji, Abdulrahman Dambazau, a jerin sabbin jakadu, da kuma Ibok Ibas, tsohon gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Rivers.

Wadannan sunaye ba su kasance cikin jerin farko da fadar shugaban kasa ta fitar a baya ba.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta takardar daga shugaban kasa a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda Tinubu ya roƙi ‘yan majalisa su gaggauta tantance su don cike muhimman kujerun diflomasiyya.

Akpabio ya tura sunayen zuwa kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar dattawa tare da umarni cewa a kammala tantancewa kuma a kawo rahoto cikin mako guda.

Tun da farko, shugaban kasa ya riga ya mika sunayen Reno Omokri, Femi Fani-Kayode da Mahmood Yakubu a matsayin jakadu.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here