NAPTIP ta dakile safarar mata 7 daga Kano zuwa Saudiyya

0
7

Hukumar Dake Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) shiyyar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da shirya fitar da mata bakwai zuwa Saudiyya domin yin aikatau.

An kamen nasa ne a ranar 2 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri cewa an ɓoye matan a wani gida a Kano cikin shirin tura su ƙasar Saudiyya.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Mohammed Habib, ya bayyana cewa matan sun ƙunshi ’yan Najeriya biyar da ’yan Nijar biyu. 

Ya ce an kai su birnin Accra dake Ghana inda aka yi musu biza tare da tanadin zuwa Saudiyya don aikin bauta.

NAPTIP ta ce an gama shirya jigilar matan ne ta filin jirgin saman Abuja a ranar 3 ga Disamba kafin jami’an ta su dakile yunkurin. An kama mutum ɗaya yayin da sauran da ake zargi da hannu a lamarin suka tsere.

Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike domin cafke sauran masu hannu wajen safarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here