Mai ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na mutanen da ke kusa da shugaban ƙasar sun taɓa nuna masa ƙyama a baya.
Bwala ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani kan ce-ce-ku-cen cewa wasu sunayen jakadu da aka gabatar ba su kamata su samu gurbin zama jakadu ba domin sun yi adawa da Tinubu a baya. Yayin wani shiri a Arise TV, Bwala ya ce Tinubu ya sha faɗa masa cewa mahaifiyar sa ta koya masa yadda ake rungumar mutanen da suka yi maka adawa.
Ya ce fadar shugaban ƙasa ta zabi yin shiru har sai Majalisar Dokoki ta kammala tantancewa, don kauce wa tasiri ko katsalandan a tsarin amincewa da jakadu. Ya kara da cewa siyasa na cike da ruɗani, kuma shugaban ƙasa yana da hurumin zabar wanda zai yi aiki da shi, ko da sun taɓa yi masa adawa.


