Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dauki matakan ladabtarwa kan wasu ma’aikata, ciki har da dakatar da biyu ba tare da biyan su albashi ba, da kuma jan kunne ga wani Alkalin Babbar Kotun Shari’a.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, hukumar ta ce matakan sun biyo bayan zaman taron ta na 88 karkashin jagorancin Babbar Alkaliya ta jihar, Dije Abdu Aboki, domin tabbatar ɗa’a da gaskiya a bangaren shari’a.
Hukumar ta gargaɗi Alkalin babbar kotun shari’a ta Dambatta, Umar Bala Musa, bisa jinkirta fitar da takardun shari’a fiye da kwanaki bakwai da kundin tsarin mulki ya tanada, duk da bincike buƙatar hakan tsawon watanni uku.
Haka kuma, an dakatar da Saifuddeen Mukhtar Abdullahi, mai muƙamin maga takarda ba tare da albashi ba, yayin da ake gudanar da binciken zargin karkatar da kudaden hadin gwiwa na ma’aikata ta hanyar yin amfani da takardu na bogi.
A gefe guda, Kamal Ado, jami’in rubuce-rubuce a Kotun Shari’a ta Kurna, ya gurfana a gaban kotun tarayya kan zargin hulda da miyagun kwayoyi, kai hari ga jami’an hukuma da kuma lalata shaidu. Shi ma an dakatar da shi ba tare da albashi ba har sai an kammala shari’ar sa.
Hukumar ta kuma sanar da janye takunkumin hana karin girma na shekara huɗu da aka saka wa Ibrahim Adamu, bayan ya kammala fuskantar dakatarwa, tare da yin nadama.


