Amurka ta sanya takunkumi ga wasu ƴan Najeriya da aka zarga da take hakkin kiristoci

0
10

Gwamnatin Amurka ta kaddamar da sabon takunkumin hana shaidar shiga ƙasar ga wasu ‘yan Najeriya da ake zargi da aikata ko tallafa wa ayyukan da ke tauye ‘yancin addini.

Marco Rubio, sakataren harkokin wajen Amurka, ya bayyana a shafin sa na X cewa matakin ya shafi duk wanda aka samu da “ba da umarni, daukar nauyi, tallafawa ko aikata laifukan da suka shafi tauye ‘yancin addini”. Ya ce wannan manufar ba ta tsaya ga Najeriya kadai ba, har da wasu kasashe da ke hukunta mutane saboda akidar addinin su.

Rubio ya ce matakin ya biyo bayan tashin tarzoma da hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya da wasu sassan duniya, wanda Amurka ke kallon hakan a matsayin cin zarafi mai tsanani.

Wasu ‘yan majalisar Amurka sun gudanar da wani taro na musamman a Washington tare da kwararru kan ‘yancin addini, domin tattaunawa kan karuwar hare-hare da ake alakantawa da tsananta wa mabiya addinin Kirista a Najeriya. Wannan binciken na gudana ne bisa umarnin Shugaba Donald Trump.

A baya-bayan nan, Chris Smith, shugaban kwamitin harkokin ketare na majalisar wakilai bangaren Afrika, ya gabatar da wani kudiri da ke shawartar kakabawa wasu mutane da kungiyoyi takunkumin hana su shiga Amurka da kuma rikr musu kadarori saboda cin zarafin ‘yancin addini.

Kudirin ya ambaci kungiyoyin MACBAN da Miyetti Allah Kautal Hore a matsayin wadanda ake zargi da aikata irin wadannan laifuka.

Sai dai MACBAN ta yi kira ga majalisar Amurka da ta janye wannan shawarar, tana mai cewa an gaza bambance tsakanin kungiyoyin miyagun ‘yan bindiga da makiyaya masu bin doka waɗanda su ma ake kashewa a rikice-rikicen tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here