Tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta labarin bogi da ke ikirarin cewa ya yi murabus saboda matsin lambar Amurka ko batun luguden wuta kan ’yan Najeriya.
Mohammed Badaru Abubakar ya bayyana cewa rubutun da ake yadawa a kafafen sada zumunta wanda ke danganta masa kalaman cewa ba zai zauna yana kallo Amurka da Shugaba Tinubu suna kai hari kan ’yan Najeriya ba rubutun ƙarya ne, kuma ba shi da alaƙa da shi..
A wani sako da ya wallafa a Facebook ranar Laraba, 3 ga Disamba, 2025, Badaru ya ce bai taɓa faɗin irin waɗannan kalaman ba, kuma babu wani wakili ko mai magana da yawun sa da ya yi irin wannan furuci.
Ya bayyana cewa an gabatar da cikakkun dalilan murabus din sa ne kai tsaye ga Shugaban Kasa, sannan aka gabatar da bayanin ga ’yan ƙasa ta hanyar kafafen yada labarai da shafukan gwamnati.
Badaru ya ce duk wani yunkuri na haɗa murabus din sa da zarge-zargen da ke tada hankali, ba gaskiya ba ne, illa ƙirƙira da gurbatar labari.


