Gwamnatin Kano zata siyo jarage mara matuƙa domin magance matsalolin tsaro

0
11

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin jihar na samar da jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin tsaro domin karfafa sa ido a yankunan iyakar Kano da Katsina. 

Ya fadi haka ne yayin ziyarar sansanonin rundunar hadin gwiwa (JTF) a Tsanyawa da Shanono, inda ya yaba wa jami’an tsaro tare da kira ga mazauna yankunan su rika ba da bayanai kan motsin ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ce ya gabatar wa Shugaban Kasa Tinubu koken da Kano ke ciki, kuma shugaban ya amsa bukatar cikin gaggawa.

Ya umurci JTF da su tabbatar da kubutar da mutanen da aka sace, yana mai cewa hare-haren da suka addabi yankunan ba za su ci gaba da kasancewa ba.

A yayin ziyarar, ya yi jaje ga iyalan wadanda aka sace, inda aka ruwaito cewa mutum 5 zuwa 10 aka yi garkuwa da su, ciki har da mace daya da ta rasa ranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here