Wata mummunar gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta hallaka ma’aurata da ’ya’yan su uku a unguwar Kofar Sauri da ke cikin garin Katsina.
Lamarin ya faru ne lokacin da iyalin ke barci, inda wutar ta fara kamawa daga rumfa kafin ta bazu cikin sauri zuwa sauran sassa, ta kuma hana su samun hanyar tsira.
Wadanda suka rasu sun haɗa da Muhammad Habibu mai shekara 35, matar sa Fatima, da ’ya’yansu Khadija, Abubakar da Aliyu.
Rahotanni sun nuna cewa Habibu ma’aikaci ne na wucin gadi a hukumar ruwa ta jihar Katsina.
Mazauna yankin sun danganta gobarar da kamawar wutar lantarki lokacin da aka kawo wuta, lamarin da ya saba haifar da matsaloli a yankin. Shaidun gani da ido sun ce kafin jami’an kashe gobara su iso, wutar ta riga ta yi mummunar barna, duk da cewa sun yi iya ƙoƙarin su.
Wasu mazauna yankin sun dora alhakin matsalar kan yawan sauyin wutar lantarki daga kamfanin KEDCO, amma kamfanin ya musanta zargin, yana mai cewa ba zai yiwu a jingina lamarin ga su ba.
Duk da cewa ba a tabbatar da ainihin musabbabin gobarar ba, al’amarin ya tayar da hankula, inda ’yan yankin ke kira da a ɗauki matakan kariya don guje wa faruwar irin haka a nan gaba.


