CBN ya ƙara yawan kuɗin da mutane zasu riƙa cirewa a ATM
Babban Bankin ƙasa (CBN) ya sanar da sabuwar doka kan cire kuɗi, inda ya ƙara iyakar cire kuɗi ta na’urar ATM zuwa Naira 100,000 a kullum, tare da Naira 500,000 ga mutum ɗaya a kowane mako.
Sabon tsarin ya fito ne a cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Talata, wanda ya maye gurbin tsauraran dokokin takaita kuɗi a hannun mutane da aka kafa a 2022. Hukumar ta ce sauyin ya yi daidai da yunƙurin rage farashin sarrafa kuɗi, magance matsalolin tsaro, da rage dogaro da tsabar kuɗi.
CBN ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin daidaita manufofin kuɗi da yanayin tattalin arzikin Najeriya.


